Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kira da hada karfi da kafada da kuma daukar duk wasu matakan da suka dace domin dakatar masu manyan laifuffukan dake shigo da miyagun kwayoyi a cikin kasashen dake shiyyar yammacin Afrika. A kwanakin baya ne a gaban 'yan majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoire a yayin wata ziyarar da ya kai wannan kasa, Goodluck Jonathan ya jaddada muhimmancin hadin kan kasashen duniya domin yaki da 'masu sana'ar mutuwa'.
'Wadannan masu sana'ar mutuwa dake shigo da kananan makaman yaki, na haddasa tashin hankali da rashin tabbas a shiyyar mu.' in ji shugaban Najeriya tare da yin Allah wadai da matsalar 'yan fashin teku dake kamari da kuma wasu miyagun ayyukan dake kawo barazana ga tsaro, kasuwanci da ayyukan tattalin arziki a wasu yankunan nahiyar Afrika.(Maman Ada)