Jiya ranar 12 ga wannan wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayar da wata sanarwa inda ya soki harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin kasar a birnin Banghazi na kasar Libya da babbar murya tare kuma da ba da umurni ga hukumomin diplomasiyar kasar dake wakilci a wurare daban daban na duniya da su dauki matakan da suka wajaba domin kara karfafa tsaronsu. Sanarwar ta nuna cewa, shugaban kasar Amurka ya riga ya bukaci gwamantin kasar da ta samar da daukacin wajababbun tallafi domin tabbatar da zaman lafiyar ma'aikatan kasar a Libya, a sa'i daya kuma, gwamnatin kasar za ta yin kakorin tabbatar da tsaron hukumomin diplomasiyar kasar a duk fadin duniya.
Kan wannan batu, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton ita ma ta bayar da wata sanarwa inda ta kai suka ga lamarin kai harin da aka yi a Libya tare da kuma nuna juyayi ga 'yan kasar Amurka da suka rasa rayuka sakamakon harin.
A wannan rana, wani jami'in gwamnatin kasar Libya ya bayyana cewa, a daren ranar 11 ga wannan wata, jakadan kasar Amurka a kasar Libya J. Christopher Stevens da sauran jami'an diplomasiya na kasar guda uku sun rasa rayuka a cikin zanga-zangar da aka yi domin la'antar kasar Amurka a birnin Banghazi na kasar.
Ban da wannan kuma, mai ba da taimako ga ministan kula da harkokin tsaron gabashin yankin kasa na ma'aikatar harkoki cikin gida ta kasar Libya Wonius Sharif ya yi taron ganawa da manema labarai a birnin Benghazi inda ya bayyana cewa, gaskiya zanga-zangar da aka yi a birnin a daren ranar 11 ga wannan wata shi ne domin nuna kiyayya ga wani fim dake bacin manzon Allah Muhammad na addinin musulunci, ba ma kawai wadanda suka shiga zanga zangar sun hada da masu dauke da makamai ba, har ma sun hada da fararen hula.(Jamila)