Kamfanin dillancin labarai ta kasar Sin Xinhua ta ba mu labari cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama a jiya Alhamis 25 ga wata ya jefa kuri'arsa da wuri a Chicago dake jiharsa ta Illinois da rana, abin da ya sa ya zama irinsa na farko da shugaba mai ci kuma 'dan takara zai jefa kuri'a da wuri da kuma kansa.
Ganin cewa saura kwanaki 12 a jiya kafin ranar babban zaben da yake takara, Obama ya isa rumfar zabe da misalin karfe 4 da minti 20 na yammacin agogon kasar, ya cika takardun da ya kamata, ya nuna takardar izininsa na tukin mota, sannan ya zabi wanda yake so a cikin 'yan takaran ta hanyar amfani da na'urar tabawa da yatsa, a cewar ofishin watsa labarai na fadar "White House".
Masu gudanar da yakin neman zaben na Obama suna ta kiran mutane da su jefa kuri'ansu da wuri kamar yadda dimbin jihohi suka fara aiwatarwa da wuri kafin ranar babban zaben. Shugaban ya yi amfani da wannan bayanin da ya yi yana kada kuri'arsa domin ba da kwarin gwiwa ga magoya baya su yi hakan.
In ji kakakin yakin neman zaben Obama lokacin wani ganawa da 'yan jarida daga cikin jirgin shugaban kasar Airforce one kan hanyarsu zuwa Richmon Virginia, Jen Psaki ta ce, "Shugaban zai jefa kuri'arsa da wuri yau a Chicago, wannan ne karo na farko da shugaba mai ci kuma 'dan takara zai jefa kuri'a da kansa kuma da wuri."
Masu yakin neman zaben Obama sun ce, zaben wuri yana da matukar muhimmanci wajen samun magoya baya sosai kafin ranar zaben domin buge 'dan takarar Republican, musamman a wasu wurare masu karfi.
Shugaba Obama da yanzu haka yake yawon neman zabe na yini biyu a wasu jihohi 8, yana rike da wasu dama fiye da 'dan takarar Republican sakamakon yawan wadanda suka yi zaben wuri. Kamar yadda mujallar "Times" ta jiya Alhamis ta wallafa ta nuna, shugaba mai ci yana gaba da mai karawa da shi a matsayin 2 da baki mutanen dake garin da yake babban fagen daga wato Ohio wadanda suka ce, sun riga sun jefa kuri'unsu.(Fatimah)