in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Uganda za ta ci gaba da kasancewa a CAR
2013-03-28 10:49:49 cri

A ranar Laraba 27 ga wata, mahukuntan kasar Uganda suka yi shelar cewa, rundunar sojin kasar dake jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, mai kunshe da sojoji kimanin 2,000 za ta ci gaba da wanzuwa a sansanoninta, domin fatattakar 'yan tawayen kungiyar nan ta LRA dake boye a Afirka ta Tsakiyar, duk kuwa da juyin mulkin da rundunar Seleka ta yi a kasar.

Karamin ministan harkokin wajen kasar ta Uganda Okello Oryem ne ya bayyana hakan ga manema labaru, yana mai cewa, rundunar sojin kasar tasa na da hurumin yin hakan, duba da cewa, tuni ta samu amincewar kungiyar AU da MDD bisa wannan kuduri. Oryem ya kara da cewa, sojin kasar tasu za su ci gaba da farautar 'yan tawayen na LRA, wadanda ke ta da kayar baya a wannan yanki, ciki hadda madugunsu Joseph Kony, sai dai idan har kungiyar AU ko MDD ta dakatar da su.

Daga nan sai ya kore batun umarnin da rundunar Seleka ta ce za ta bayar, na ficewar dukkanin rundunonin sojin ketare dake kasar, yana mai cewa, Seleka na gudanar da haramtacciyar gwamnati ne a kasar ta Afirka ta Tsakiya, don haka ba ta da zarafin baiwa dakarun Ugandan wani umarni.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China