in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a mutunta halin da kasashe daban-daban ke ciki lokacin bunkasa tattalin arzikin kiyaye muhalli
2011-06-03 14:03:29 cri

Ranar Alhamis 2 ga wata a birnin New York hedkwatar MDD, yayin da Du Ying mataimakin diraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya halarci muhawara kan batun tattalin arzikin kiyaye muhalli na babban taron MDD na 65, ya lura cewa, bunkasa irin wannan tattalin arziki yana bukatar a mutunta halin da kasashe daban-daban ke ciki da zummar kawar da talauci, ciyar da samun ci gaba mai dorewa gaba.

A gun muhawarar, Du Ying ya gabatar da ra'ayoyi hudu, wato ya kamata a mai da hankali kan kawar da talauci da kuma sa kaimi ga samun ci gaba mai dorewa, mutunta halin da kasashen daban-daban ke ciki, daukar nauyin baki daya tare da fahimtar bambance-bambance, kafa wani tsarin tattalin arzikin duniya cikin adalci.

Du Ying ya ce, a cikin shekaru 5 masu zuwa, Sin za ta yi kokarin samun ci gaba mai dorewa cikin lumana, da kyautata zaman rayuwar jama'a tare da mai da muhimmanci kan aikin yin tsimin makamashi da rage fitar da kayayyakin gurbata muhalli da kara bunkasa karfin samarwa yadda ya kamata.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China