in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan gwamnatin Zambiya za ta daidaita batun kamfanin mahakar kwal na jarin kasar Sin bisa doka
2013-02-22 19:51:36 cri
Game da kudurin da gwamnatin kasar Zambiya ta tsai da na karbar ikon tafiyar da kamfanin mahakar kwal na Collum na jarin kasar Sin, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar Jumma'a 22 ga wata a nan Beijing cewa, kamfanin ya yi rajista a Zambiya. Ya kamata a daidaita batutuwan da abin ya shafa bisa dokokin kasar ta Zambiya. Gwamnatin Sin tana fatan tare da imani cewa, gwamnatin Zambiya za ta daidaita batutuwan da lamarin ya shafa bisa dokoki yadda ya kamata, kuma za ta kiyaye halaltattun hakkokin masana'antu.

An labarta cewa, ministan ma'adinai na Zambiya ya sanar a ran 20 ga wata da cewa, gwamnatin kasar za ta karbi ikon tafiyar da mahakar kwal ta Collum daga wannan rana, saboda mahakar kwal din nan ta dade tana fama da matsaloli da dama a fannonin hako kwal da gurbata muhalli. Sa'an nan kuma ta soke iznin da aka bai wa kamfanin na hako kwal a sauran wuraren hakar kwal guda 3 da ke kasar.

Dangane da lamarin, Hong Lei ya nuna cewa, har kullum gwamnatin Sin na tsayawa kan yin hadin gwiwa da kasashen waje bisa ka'idar samun moriyar juna da nasara tare, ta kuma bukaci kamfanonin kasar Sin da 'yan kasuwan da suka zuba jari a ketare da su nuna gaskiya da rikon amana, bin dokoki yadda ya kamata, da gudanar da harkokin kasuwanci bisa ka'idojin da abin ya shafa, sa'an nan su yi kokarin kara ba da gudummawa wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa na wurin da suke zaune tare da inganta rayuwar mazauna wurin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China