Sanusi ya bayyana hakan ne ranar litini yayin ganawa da manema labarai a kan matsaya da aka cimma a ganawar kwamitin manufofin kudade(MPC).
Shugaban babban bankin wanda shi ne ya jagoranci ganawar ya ce an kara yawan kudin gangar man daga dalar Amurka 75 zuwa 79 kuma hakan na iya kawo matsala ga manufofin hana haurawar farashin kayayyaki da ma sauran manufofi da suka shafi hada hadar kudi a shekarar 2013 din baki daya.
Wannan shi ne karo na 7 da kwamitin ya tsayar da farashin kudin ruwa kan kashi 12 cikin dari saboda ba za'a iya ragewa zuwa kasa da hakan ba bisa la'akari da hauhawar farashin kayayyaki yanzu haka a kasar. END