in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ce matsayinta kan zirin koriya ya dace
2013-04-24 20:00:11 cri
A ranar Talata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Yun Byung-se,inda ya ce matsayin da Sin ta dauka kan zirin Koriya ya dace.

Wang ya ce, abu mai muhimmanci shi ne, dukkan bangarorin su yi hakuri, daukar matakan da suka dace, rage zaman dar-dar kana su koma kan teburin sulhu.

Mr Yun ya mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda bala'in girgizar kasar da ta abku a lardin Sichuan ta shafa, yana mai bayyana cewa, Koriya ta Kudu tana son bayar da tallafi ga wadanda wannan bala'i ya shafa.

A jawabinsa Mr Wang ya ce Sin da Koriya ta Kudu muhimman kasashe ne a shiyyar, kuma dangantakar kasashen biyu za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya a zirin Koriya da kuma shiyyar baki daya tare da taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China