Kwamitin kiwon lafiya da shirin kayyade haihuwa na kasar Sin ya bayyana cewa, an riga an dauki matakan sa ido kan duk wadanda suka taba yin mu'ammala da wadanda suka kamu da cutar, a cikinsu kuma, an samu mutum guda daya da ya nuna alamar kamuwa da mura, amma ba ta murar tsuntsaye nau'in H7N9 ba, yayinda sauran suke cikin lafiya.
Kawo yanzu, cutar tana ci gaba da yaduwa, amma han yanzu ba wanda ya kamu da ita ta hanyar samun yaduwa daga mutum zuwa mutum ba.
A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, yawan mutanen da suka kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 ya karu. A sabili da haka, ake kara kokarin yin rigakafi da ba da jiyya kan wannan cuta a wurare daban daban na kasar Sin.
Daga ranar Asabar 6 ga wata, za a dakatar da sayar da tsuntsaye masu rai a birnin Shanghai, tare da rufe kasuwannin sayar da tsuntsaye.
A sa'i daya, an riga an dauki kwararran matakai a birnin Beijing, lardunan Guangdong, Yunnan, Hubei, Sichuan da sauransu, inda ba a samu wadanda suka kamu da cutar ba tukuna, domin kara karfin yin rigakafi.
Gwamnatocin mataki-mataki da yawa sun yi alkawari ga kafofin yada labaru cewa, ko kadan ba za su boye labari dangane da cutar ba. (Fatima)