Bisa labarin da aka bayar, an ce, daya daga cikin mutanen hudu mai aikin fidan kaza ne, kuma dukkan mutanen 4 da suka kamu da cutar suna jin zazzabi, ciwon kai, tare kuma da yin tari.
Ya zuwa yanzu dai, ba a gano wata alaka tsakanin mutanen hudu ba dangane da yaduwar cutar, kana mutanen dake zama tare da su ba sa jin zazzabi ko kuma yin tari ya zuwa yanzu. (Zainab)