Majalisar dokokin kasar Somaliya ta amince da sabuwar gwamnatin kasar bisa yawan kuri'un da firaminista Abdi Farah Shirdon ya gabatar a ranar Talata.
Bisa mambobi 225 da majalisar dokokin take kunshe da su, 'yan majalisa 219 sun jefa kuri'un amincewa da wannan sabuwar gwamnati, yayin da uku suka jefa kuri'un kin amincewa, sannan uku suka janye jikinsu, in ji shugaban majalisar dokokin, mista Mohamed Sheikh Osman.
Firaminista Shirdon ya gabatar da jadawalin aikin gwamnatinsa bisa shekaru hudu masu zuwa a gaban 'yan majalisar kafin wannan zabe, tare da jaddada cewa, gwamnatinsa za ta mai da hankali sosai kan muhimman batutuwan dake ciwa 'yan kasar Somaliya tuwo a kwarya, ta yadda za ta yaki matsalar rashin tsaro, ayyukan 'yan fashin teku da kuma masu tsatsauran ra'ayi, ta hanyar karfafa matakan tsaro da kayayyakin aiki ga gwamnatin kasar.
Sabuwar gwamnatin kasar Somaliya dai na fuskantar babbar matsalar maido doka da oda a wasu yankunan kasar dake hannunta da kuma fadada ikonta a duk fadin kasar da aka lalata a tsawon shekaru masu yawa. (Maman Ada)