A ranar Laraba 7 ga wata ne dai, kwamitin tsaro na MDD ya amince da kudurin neman karin wa'adin ayyukan samar da zaman lafiya da dakarun hadin gwiwa na kungiyar AU ke gudanarwa a kasar Somaliya zuwa watan Maris na shekarar badi.
Wannan dai na da nufin baiwa rundunar ta AMISOM damar daukar dukkanin matakan da suka dace, don rage barazanar da kungiyoyin 'yan tada kayar baya ke yi ga wanzuwar halastacciyar gwamnati a kasar. Haka zalika, ana fatan matakin zai ba da damar komawa teburin shawarwari da kuma zartas da shirin yafiya tsakanin bangarorin da rikicin kasar ya shafa.
Bugu da kari, kwamitin ya amince da kara wasu masu sa ido farar hula guda 50, da za su gudanar da aiki na wani 'dan lokaci, cikin tawagar tsare-tsare ta MDD, dake ba da tallafi ga rundunar ta AMISOM.
Ita dai wannan runduna ta AMISOM, kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU ce ta kafa ta cikin watan Janairun shekarar 2007, musamman don murkushe ayyukan ta'addanci dake barazana ga dorewar kasar ta Somaliya, tare da tabbatar da aniyar gudanar da shirin yafiya a dukkanin fadin kasar dake gabashin Afirka.(Saminu)