in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya tana fatan koyon fasahohin da Sin ta samu wajen raya makamashi cikin dogon lokaci
2012-11-08 16:29:55 cri
Ministan kula da harkokin haka ma'adinai da raya harkokin karafa na kasar Nijeriya Musa Mohammed Sada ya furta a jiya 7 ga wata a nan birnin Beijing cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, cigaba da Sin ta samu wajen raya makamashi da kiyaye muhalli ya burge shi sosai, kuma Nijeriya tana kokarin koyon fasahohin da Sin ta samu wajen bincike da haka ma'adinai, gami da cin moriyar fasahohin da Sin ta samu wajen kulawa da ma'adinai.

Sada ya fadi haka ne yayin da yake zantawa da wakilinmu a yayin taron kasa da kasa game da hako ma'adinai na kasar Sin na shekara ta 2012. Ya ce, taron ya samar da wani dandalin yin shawarwari tsakanin ministocin haka ma'adinai da manyan jami'an kamfanoni masu harkar hako ma'adinai na Sin da na kasashen waje, kuma ta wannan hanya ce, jami'an gwamnatoci da kamfanoni za su yalwata fahimtar juna da cimma daidaito, har ma da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Ta hanyar ziyartar masana'antun haka ma'adinai, kasar Nijeriya tana fatan koyon fasahohin da Sin ta samu, da kuma sa kaimi ga bunkasa harkokin ma'adinai cikin daidaituwa, da kawo alheri ga jama'a.

Haka kuma, Minista Sada ya ce, a cikin 'yan shekaru nan, masana'antu masu haka ma'adinai da dama sun je kasar Nijeriya, kuma sun kulla kyakkyawar hulda mai kyau da mazaunan wurin da ke da albarkatun ma'adinai. Bugu da kari, wadannan masana'antu sun sauke alhakin da ke wuyansa, inda suka gina hanyoyin mota, makarantu da asibitoci, kuma abin da ya samu karbuwa a wurin matuka. Sabo da haka, Nijeriya take kira tare da maraba da manyan kamfanoni masu haka ma'adinai da su je kasar Nijeriya, don raya wannan sana'a.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China