in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan man fetur da Nijeriya take samarwa ya ragu
2012-11-19 17:07:15 cri

Rahoton wata-wata da hukumar makamashi ta kasa da kasa ta bayar kwanan baya, ya bayyana cewa, a cikin watan Oktoba na shekarar bana, saboda bala'in ambaliyar ruwa da matsalar satar man da ake fuskanta, an samu raguwar man fetur din kasar Nijeriya take samarwa a kowace rana zuwa ganga miliyan 1.95, wanda ya ragu matuka cikin shekaru biyu da suka gabata.

Rahoton ya ce, Nijeriya na fuskantar kalubaloli da dama wajen kara samar da man fetur, ciki har da koma bayan masana'antun man fetur cikin dogon lokaci, rashin samu jari, matsalar satar man fetur da sauransu. Ban da haka, Amurka wadda ta kasance kasar da ta fi yawan shigo da man fetur daga Nijeriya a yanzu haka tana kokarin kara yawan man fetur da take samar da kanta, lamarin da ya sanya kasar Nijeriya bukatar gano sabuwar kasuwa domin fitar da man fetur din ta, idan ba haka ba, sana'ar man fetur ta kasar za ta fuskanci kalubale mai tsanani a nan gaba.

Kididdigar da kungiyar OPEC ta kasashe masu fitar da man fetur zuwa ketare ta bayar ta nuna cewa, yawan man fetur da aka gano a karkashin kasa a Nijeriya ya kai ganga biliyan 37.2, wanda ya kai kashi 29.32 bisa dari, na kasashe Afrika gaba daya, kuma matsayi na biyu a nahiyar Afrika (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China