Bisa labarin da aka samu, an ce, kamfanin SINOPEC zai sayi hakkin da yawansu ya kai kashi 20 cikin 100 na haka man fetur a yankin OML mai lamba 138 na kamfanin TOTAL, amma ya zuwa yanzu, gwamnatin da abin ya shafa ba ta amince da wannan yarjejeniya ba tukuna.
Yanki mai arzikin man fetur na OML mai lamba 138 yana cikin yankin Niger-Delta na yankin tekun Nijeriya da ke yammacin Afrika, kuma fadinsa ya kai murabba'in kilomita 906, kamfanin Total ya mallaki hakkin hakar man fetur a wannan yanki da yawansu ya kai kashi 20 cikin 100, kuma an kiyasta cewa, za a samu man fetur da yawansu ya kai ganguna miliyan 100 a yankin, tun lokacin da aka fara haka man fetur a karshen watan Febrairu na bana, ana gudanar da aiki yadda ya kamata, kuma ya zuwa yanzu, a kan samar da man fetur da yawansu ya kai ganguna dubu 24 a kowace rana daga yankin.
Wani jami'in kamfanin SINOPEC ya bayyana cewa, SINOPEC a shirye take don yin hadin gwiwa da abokan aiki na kasashen duniya, a karkashin tushen samun moriyar juna da cimma nasara tare, za a raya harkokin haka man fetur a kasashen waje tare. A wannan gami kamfanin SINOPEC da TOTAL suka cimma yarjejeniyar haka man fetur a kasar Nijeriya, hakan zai iya samar da gurbataccen man fetur ga wannan yanki.(Bako)