Kungiyar ciniki ta duniya WTO ta kammala nazarin manufofin cinikayya karo na hudu na kasar Sin a ran 14 ga wata a birnin Geneva. Mahalarta taron sun tattauna kan tasiri da bunkasuwa da manufofin tattalin arzikin kasar Sin suka kawowa tattalin arzikin duniya da sauran kasashe mambobin kungiyar, tare da amincewa da kokarin da Sin ta yi, kuma tana fatan Sin ta kara taka rawa a fannin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa.
Yayin nazarin na tsawon kwanaki biyu, tawagar kasar Sin a karkashin jagorancin Yu Jianhua, mataimakin ministan ciniki na kasar Sin, ta tattauna sosai da mambobin kasashen WTO kan wasu manyan sassan tattalin arziki, da bunkasuwar tattalin arziki da ciniki, da kuma manufofin da abin ya shafa da kasar Sin ta dauka cikin shekaru biyu da suka wuce. Ban da wannan kuma, wakilan kasar Sin sun amsa tambayoyin da aka gabatar musu.(Amina)