in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta amince da shigar Rasha
2011-12-17 17:28:41 cri
Taron ministocin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) a ranar 16 ga wata ya amince da shigar kasar Rasha cikin kungiyar, abin da ya dasa aya ga yunkurin kasar ta Rasha cikin shekarun 18 da suka wuce wajen neman shiga kungiyar.

Babban darektan kungiyar WTO, Pascal Lamy ya bayyana cewa, shigar Rasha cikin kungiyar wani muhimmin al'mari ne ga kasar tare kuma da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori da dama. A cewarsa, daga nan kungiyar tana iya cimma buri na harkokin ciniki da ya kai kashi 97% a duniya. An ce, Rasha za ta zama mambar kungiyar nan da kwanaki 30 masu zuwa bayan da aka amince da yarjejeniyar, kuma bisa ga yarjejeniyar, Rasha za ta rage kudin kwastan da take sanyawa daga 10% zuwa 7.8%.

A wannan rana, shugaban kasar Rasha, Dmitry Medvedev ya mika sako na godiya ga taron kan yadda aka karbi kasarsa cikin kungiyar, kuma ya yi hasashen cewa, Rasha da abokan hadin gwiwarta dukkansu za su amfana daga shigarta cikin kungiyar. Ya kara da cewa, kungiyar WTO tana iya tabbatar da dorewar tattalin arzikin duniya, kuma Rasha a shirye take ta ba da nata taimako.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China