in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko shan sinadarin Calcium da yawa yana da amfani ga lafiyarka?
2019-04-23 08:15:44 cri
A halin yanzu shan sinadarin Calcium ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma. Amma mutane da yawa ba su san cewa, bukatun mutane na shan sinadarin Calcium sun sha bamban sosai sakamakon shekarunsu na haihuwa. Musamman ma idan kananan yara, suka sha sinadarin Calcium fiye kamar yadda suke bukata, to, mai yiwuwa hakan zai iya haifar da kumburin jiki, yin gumi da yawa, karancin sha'awar cin abinci, yawan tashin zuciya, kasa yin bayan gida, da matsalar narkar da abinci, da ma haddasa matsalar yawan sinadarin Calcium a cikin fitsarin dan Adam. Haka zalika kuma, idan kananan yara suka shan sinadarin Calcium fiye da yadda jikinsu ke bukata, yiwuwa hakan ya hana kwakwalwarsu ta girma yadda ya kamata, ta yadda hakan zai iya hana kananan yara girma yadda ya kamata.

Kwararru sun yi nuni da cewa, kamata ya yi a sha sinadarin Calcium bisa bayanan likitoci. Jariran 'yan kasa da watanni 7 a duniya, ba sa bukatar sinadarin Calcium da ya kai milligram dari 3 zuwa dari 4 a ko wace rana, kana kananan yara da shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 5 da haihuwa ba suna bukatar sinadarin Calcium milligram dari 6 zuwa dari 8 ne kawai a ko wace rana, wadanda shekarunsu suka wuce 4 amma ba su kai 15 a duniya ba kuma suna bukatar sinadarin Calcium milligram dari 8 zuwa dubu 1 ne kawai a ko wace rana. Baligai kuma fa? An ba da shawarar cewa, mata da maza baligai bai kamata su sha fiye da milligram dubu 2 na sinadarin Calcimun a ko wace rana ba. Watakila shan sinadarin Calcium fiye da yadda muke bukata zai kawo cikas ga shiga wasu sinadarai marasa yawa cikin jikinmu, kana kuma zai haifar da matsalar duwatsu a koda. Har ila yau kuma sakamakon yadda hanta da kodar tsofaffi ba sa aiki yadda ya kamata, ya sa jikin tsoffafin ba su iya shigar da magunguna da sarrafa su kamar yadda matasa suka yi, shi ya sa ya zama tilas tsoffafin su mai da hankali sosai wajen shan sinadarin Calcium, ya kamata su sha sinadarin Calcium milligram dubu 1 da dari 2 zuwa dubu 1 da dari 5 ne kawai a ko wace rana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China