in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kanana yara da ke fama da cutar Autism ba su sha'awar launin rawaya
2019-04-01 08:54:12 cri

Masu nazari da suka fito daga kasashen Japan da Faransa sun gano a kwanakin baya cewa, kananan yara wadanda suke fama da cutar Autism ba su sha'awar launin rawaya. Watakila nazarin zai taimaka wajen kyautata yanayi daga fannin launuka don dacewa da kananan yara masu fama da cutar ta Autism.

Jikunan kananan yara masu fama da cutar ta Autism su kan ki yanayin da suke kasancewa. Alal misali, irin wadannan yara su kan ji kara mai karfi, duk da cewa, karar ba ta da karfi ko kadan a kunnen masu koshin lafiya. Kana kuma in an taba fatansu, su kan ji ciwo sosai, ko da an taba su ne a hankali. Masu nazari daga jami'ar Kyoto ta kasar Japan da kuma jami'ar Rennes ta kasar Faransa sun gudanar da wani nazari kan lamarin, a kokarin ganin ko kananan yara masu fama da cutar Autism suna kin jinin wasu launuka, ko a'a.

Masu nazarin sun gayyaci kananan yara maza 29 da shekarunsu suka wuce 4 amma ba su kai 18 a duniya ba mazauna birnin Rennes da kuma takwarorinsu masu koshin lafiya 38 domin shiga nazarin. Sun tantance sha'awarsu kan launukan ja, rawaya, kore, shudi, kasa-kasa da ruwan hoda. Idannun dukkan wadannan kananan yara maza ba su da wata matsala ko kadan.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, dukkan wadannan kananan yara maza sun fi sha'awar launukan ja da shudi. A cikin sauran launuka guda 4 kuma, masu koshin lafiya suna sha'awar launin rawaya, amma ba su son launin kasa-kasa, yayin da masu fama da cutar ta Autism suka fi sha'awar launin kasa-kasa, a maimakon launin rawaya.

Masu nazarin suna ganin cewa, launin rawaya, launi ne mafi haske a cikin launuka guda 6 da suka gudanar da nazarinsu a kai. Watakila kananan yara masu fama da cutar Autism suna ganin cewa, launin rawaya yana da haske fiye da yadda suke iya jurewa. Idan kananan yara masu fama da cutar Autism suna rayuwa cikin yanayin da ya matsa musu sosai, ciki had da launuka, zai kawo illa ga zaman rayuwarsu. Don haka, masu nazarin sun yi fatan cewa, yayin da ake kulawa da kananan yara masu fama da cutar Autism, dole ne a mai da hankali kan launukan da ke kewaye da su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China