in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kiwon dabbar gida kamar kare yana taimakawa kiwon lafiyar jarirai
2019-03-11 14:07:55 cri


Wasu kan kori dabbobin gidansu wani wuri na daban yayin da suke fatan samun ciki, saboda suna damuwa da cewa, dabbobin gida suna kawo illa ga lafiyar jarirai. Amma wani sabon nazari ya nuna mana cewa, kiwon dabbobin gida kamar karnuka yana amfana wa lafiyar jarirai. Barazanar kamuwa da cututtukan borin jini da ciwon kiba da jariran da suke rayuwa tare da karnuka suke fuskanta, ba ta da yawa.

Masu nazari daga jami'ar Alberta ta kasar Canada sun kaddamar da rahotonsu da cewa, sun tantance kashin wasu jarirai 'yan kasar Canada, da ko suna rayuwa da dabbobin gida ko a'a. Sun gano cewa, tun bayan da mata suka samu ciki har zuwa cika watanni 3 da haihuwar jarirai, idan ana kiwon dabbobin gida kamar karnuka da sauran dabbobin gida masu gashi a gida, yawan wasu nau'o'in 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki guda 2 ya kan karu cikin hanjin jariran. Wadansu 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki guda 2 suna iya rage barazanar kamuwa da cututtukan borin jiki da ciwon kiba da kananan yara suke fuskanta.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, watakila dalilin da ya sa haka shi ne domin akwai wadansu 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki a cikin gashin dabbobin gida da kuma hannunsu. Jarirai suna iya samun wadannan 'yan kwayoyi kai tsaye ta hanyar taba su, kana kuma suna iya samun su ta hanyar taba mahaifansu wadanda suka shafa dabbobin gida. A baya, an gano cewa, mahaifa mata kan bai wa jariransu 'yan kwayoyi da suke da su, yayin da suka haife su. Don haka masu nazarin sun yi nuni da cewa, idan masu juna biyu suka shafa karnuka da sauran dabbobin gida yayin da suke da ciki, ko da sun kore su kafin sun haihu, suna iya bai wa jariransu wadannan 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki ta hanyoyin da muka ambata a baya.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, idan wasu ba su so su kiwo karnuka ko sauran dabbobin gida, amma suna fatan kara yawan wasu 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki a jikin jariransu, to, watakila za a harhada wasu magungunan da ke kunshe da 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki a nan gaba. Shan irin wadannan magunguna kai tsaye ya yi kama da yadda ake kiwon karnuka da sauran dabbobin gida. Masu nazarin suna ganin cewa, wannan ba wani mafarki ne kawai ba ne, yanzu haka wasu kamfanonin harhada magani suna harhada magungunan da ke kunshe da 'yan kwayoyi masu amfanawa jiki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China