in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko maganin Aspirin yana iya yaki da ciwon sankara?
2019-04-12 15:02:06 cri

Masu karatu, ko kun taba shan magani fiye da yadda likita ya kayyade domin shawo kan cututtuka? Ko kuna shan abubuwa masu gina jiki domin kiwon lafiya? Hakika dai, akwai rashin fahimta a wasu fannonin rigakafin cututtuka da kuma kwion lafiya. Yau bari in gabatar muku wasu daga cikin wadannan fannoni.

Ko Maganin Aspirin yana iya maganin ciwon sankara?

Maganin Aspirin yana da tsawon shekaru fiye da dari daya. Ana amfani da shi ne wajen rage zafin jiki, kau da ciwo da maganin kunburi, kana kuma ana shan maganin ne wajen yin rigakafin da kuma shawo kan wasu cututtukan jijiyoyin zuciya.

A shekarun baya da suka wuce, ana jita-jita a kan yanar gizo ta Internet cewa, maganin na Aspirin yana iya yin rigakafin ciwon sankara. Nan da nan wannan karamar kwayar magani ta zama maganin da ke iya shawo kan ko wace cuta wadda mutane da yawa suke gwagwarmayar samu. Amma duk da haka, mutane masu yawa ba su san cewa, shan maganin na Aspirin fiye da yadda likita ya kayyade, na iya haifar da mummunar illa ga lafiyarka!

Kwararru masu ilmin likitanci sun yi nuni da cewa, maganin Aspirin yana amfani wajen hana taruwar wani abu a cikin jini dake sa jini ya bushe in an samu rauni wato blood cells a Turance. Idan wani ya sha maganin fiye da yadda likita ya gaya masa kuma cikin dogon lokaci, mai yiwuwa ya kawo illa ga lafiyarsa, har ya kai mutum dab da bakin mutuwa. Alal misali, idan mutanen da suke fama da gyambon tumbi da gyambon hanji suka sha maganin Aspirin, watakila tumbinsu da hanjinsu su rika fid da jini ko kuma tumbinsu da hanjinsu su fashe. Kana kuma, wasu masu fama da asma su kan kamu da kuraje, ko kumburin makogwaro, ko ya tayar musa da asma sosai idan suka sha maganin na Aspirin. Har ila yau kuma, idan tsawon lokaci da masu juna biyu suka dauka suna samun ciki bai wuce watanni 3 ba, amma suka sha maganin Aspirin, zai kawo illa ga lafiyar 'yan tayinsu, haka zalika, idan sun dauke dogon lokaci suna shan maganin, sai iya dakatar da haihuwarsu, tare da haddasa barazanar fid da jini. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China