in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'adar shan abin sha mai matukar zafi ta kara barazanar kamuwa da ciwon sankara
2018-07-16 16:07:29 cri

Assalamu Alaikun, jama'a masu sauraro. Sashen Hausa ke gabatar muku da shirin "Lafiya Uwar Jiki". Kuma ni ce Tasallah ke muku marhabin a wannan zaure daga birnin Beijing, inda zan gabatar muku wasu muhimman bayanai game da yadda za mu kara kula da lafiyarmu yadda ya kamata. (music)

Kwanan baya, kwalejin nazarin ciwon sankara na kasa da kasa karkashin shugabancin hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ya ayyana cewa, al'adar shan abin sha mai matukar zafi zai sa karuwar barazanar kamuwa da ciwon sankara. Yana ganin cewa, watakila shan kofi, ruwan shayi da sauran abubuwan sha da zafinsu ya wuce digiri 65 a kullum zai haddasa ciwon sankaran makogwaro.

A cikin sanarwar da kwalejin nazarin ciwon sankara na kasa da kasa ya bayar, ya bayyana cewa, kwararru 23 daga kasashe guda 10 sun auna barazanar kamuwa da ciwon sankara da abin sha mai matukar zafi yake haddasawa, bisa rahotannin nazari da aka fitar a halin yanzu. Suna kuma ganin cewa, akwai shaidan dake nuna cewa, akwai wata alaka a tsakanin kamuwa da ciwon sankaran makogwaron dan Adam da kuma shan abu mai matukar zafi, wanda zafinsa ya wuce digiri 65.

Kwalejin ya kara da cewa, wasu nazarce-nazarce da aka gudanar a kasashen Iran, Sin, Turkey da kasashen kudancin nahiyar Amurka, inda aka saba shan abu mai zafi, sun nuna cewa, kullum mazauna wurin masu yawa su kan sha ruwan shayi da zafinsa ya wuce digiri 70. Idan har zafin ruwan shayi ya karu, to barazanar kamuwa da ciwon sankaran makogwaro za ta karu. Ban da haka kuma, nazarin da aka gudanar kan beraye shi ma ya shaida cewa, watakila shan abu mai matukar zafi zai kara wa berayen barazanar kamuwa da ciwon sankara.

Sanarwar ta yi bayanin cewa, ciwon sankaran makogwaro ya zama na 8 a cikin munanan cututtukan sankara da mutane su kan kamu da su a duniya. Mutane da yawa sun mutu sakamakon ciwon. A shekarar 2012, mutane kimanin dubu 400 ne suka rasa rayukansu a duniya baki daya sakamakon ciwon sankaran makogwaro. Kasar Sin tana fama da ciwon sankaran makogwaro sosai.

Masu nazarin sun jaddada cewa, muhimmin abin da ya haddasa ciwon sankara shi ne abin sha mai zafi, a maimakon nau'o'in abubuwan sha da a kan sha kullum.

Kwalejin nazarin ciwon sankara na kasa da kasa yana karkashin laimar hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO. Kuma an kafa shi ne a shekarar 1965, yana kuma taimakawa nazarin da ake yi kan ciwon sankara da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China