in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila yawan cin abincin da aka sarrafa sosai zai kara barazanar kamuwa da ciwon sankara
2018-07-10 10:26:46 cri

Kwanan baya, masu nazari daga kasar Faransa sun wallafa wani rahoton nazari a mujallar ilmin likitanci ta kasar Birtaniya, inda suka nuna cewa, watakila cin yawan cin abincin da aka sarrafa sosai zai kara barazanar kamuwa da ciwon sankara, musamman ma ciwon sankarar mama.

An raba abinci zuwa sassa hudu bisa yadda aka sarrafa su, wato abincin da ba a sarrafa ba, da sukari, gishiri, man shanu da sauran abubuwan da ake bukata na girki, da abincin da aka dafa da wadannan nau'o'in abinci biyu da muka ambata a baya, da kuma abincin da aka sarrafa su sosai, kuma aka hada kayayyakin miya masu kamshi a ciki don kara dandanon abincin. Cakulan, biskit, abincin sha da aka hada da kayan miya mai kamshi don kara dandano, daskararren abinci da dai sauransu dukkansu abinci ne da aka sarrafa su sosai.

Masu nazari daga kwalejin nazarin kiwon lafiya da ilmin likitanci na kasar Faransa, kwalejin nazarin aikin gona na kasar Faransa sun gudanar da nazari kan baligai dubu 105 daga shekarar 2009 zuwa 2017, wadanda matsakaicin shekarunsu ya kai 43 a duniya, dangane da yadda su ke cin abinci a kullum da kuma lafiyarsu. A cikin wannan lokaci, wasu dubu 2 da dari 2 da 28 sun kamu da ciwon sankara, ciki had da wasu dari 7 da 39 da suka kamu da ciwon sankarar mama.

Masu nazarin sun yi la'akari da shekarun wadannan mutane a duniya, ko sun sha taba ko giya ko a'a, yadda suke motsa jiki, ilmin da suka samu da dai sauransu, a karshe dai, sun gano cewa, idan yawan abincin da aka sarrafa su sosai ya karu da kashi 10 cikin dari bisa jimillar abincin da a kan ci a zaman yau da kullum, to, barazanar kamuwa da ciwon sankara da ake fuskanta za ta karu da kashi 12 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, yawancin abincin da aka sarrafa su sosai ba sa kunshe da abubuwa masu gina jiki da yawa. Kuma cin nau'in irin wannan abinci fiye da kima ya kan haddasa karuwar kiba ga dan Adam. Tuni aka tabbatar da cewa, kiba, wata babbar matsala ce da ke haddasa karuwar barazanar kamuwa da ciwon sankara. Yayin da aka sarrafa abinci, ko soya wa, ko gasa wa, nan da nan a kan samu sabbin abubuwan da suke haddasa ciwon sankara.

Masu nazarin sun jaddada cewa, akwai bukatar ci gaba da gudanar da nazari kan karin mutane domin tabbatar da sakamakon nazarinsu, ta yadda za a kara sanin alakar da ke tsakanin mabambantan batutuwan da suka shafi abincin da aka sarrafa su sosai da kuma ciwon sankara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China