Slm. Ina mai gabatar muku da sakon taya murnar cikin shekaru 75 da kafuwar Radiyan kasar Sin (CRI). Babu shakka gidan Radiyan kasar Sin kwalliya ta biya kudin sabulo tare da cimman manyan nasararo masu yawa bisa makasudun kafa gidan Radiyan kasar sin cri. A cikin shekaru 75 da kafuwar Radiyo kasar Sin gidan Radiyon da ma'aikatansa sun gudanar da aiyuka masu yawan gaske wayanda ke faiyace kasar Sin tare da gabatar da labaru da rahotanni masu karin haske adangane da hakikanin abun suke faruwa a kasar Sin da Afirka da ma duniya. Babu shakka, gidan Radiyan kasar Sin da ma'aikatansa sun bada muhimmiyar gudumowa wajen kara wayin kai ga milyoyin masu sauraren shirye-shiryen cri masu farin jini a fadin duniya, yayinda gidan Radiyan cri ke samu habaka sannu a hankali inda cri suke watsa shirye-shirye a cikin harsuna kasa da kasa fiye da 40. Kana gidan Radiyon cri suna kyautata mu'amularsu da masu sauraronsu a fadin duniya inda suke shirya wa masu sauraronsu gasar kacici-kacici loto-loto dan kyautata wa masu sauraro da kuma auna fahimtar masu sauraro game kasar Sin da kuma shirye-shiryensu.
Muna fata za ku kammala bukukuwa lafiya, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji
Gashua.