KO shakka babu, sabon jakadan kasar Sin ya kama aiki Yau a ofishin jakadancin kasar Sin a Abuja. Mr Zhou Pingjian ya gana da shugaban Nakeriya Muhammadu Buhari a ofishinsa domin sanar da shi kama aiki. Wannan abu ne mai kyau, kuma muna fata wannan sabon jakada zai dora gini a kan kwakkwarar tubalin da tsohon jakadan ya aza wajen kara dankon zumunci da fahimta a tsakanin kasashenmu biyu. Muna kuma yi masa fatan alheri a yayin zamansa a Najeriya.
Daga malam Salisu Dawanau a Abuja, tarayyar Nijeriya