Babu shakka, rasuwar tsohon shugaban kasar Cuba mr. Fidel Castro, babban rashi ne ga al'ummar kasar Cuba da ma daukacin kasashen Latin Amurka kana babban rashi ne ga manyan abokan kasar Cuba irinsu kasar Sin da dai sauran kasashe da nahiyoyi, masamman ma nahiyarmu ta Afirka inda marigayi Mr. Castro ya bada taimako ta fannin ilmi da kuma kokarin da ya yi wajen ganin kasashenmu na Afirka sun samu yancinsu a zamanin da kasashe yan mulkin mallaka daga yammacin turai suka mamaye kasashenmu na Afirka dan yi musu mulkin mallaka.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.