Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Ina farin cikin sanar da ku cewa, na samu labarin bude taron kasa da kasa kan fusahar yanar gizo karo na 3 a birnin Wuzhen na lardin Zhejiang a yau Laraba 16 ga watan Nuwamba a shafin ku na crihausa.com
Hakika wannan taro ya zo kan gaba, wato a daidai lokacin da ya dace bisa la'akari da irin barazanar da masu amfani da fusahar yanar gizo ke fuskanta daga masu yin kutse cikin adireshin e-mail na daidaikun mutane da kuma rumbun adana bayanai na hukumomi da ma'aikatun gwamnati daban daban. Ga kuma matsalar aikata zamba ta hanyar amfani da fusahar ta yanar gizo wacce ke karuwa sannu a hankali.
Daukan nauyin shirya wannan muhimmin taro da kasar Sin ta yi a birnin Wuzhen, ko shakka babu ya bayyana irin muhimmancin da kasar ke dorawa kan batun yanar gizo da tsaronsa. A cikin wannan shekara ta 2016 wasu matasa biyu Sinawa mace da namiji sun rasa rayukan su sakamakon kasa jure bakin cikin zambatar su kudi da a ka yi ta hanyar yanar gizo, lamarin da ya tayar da hankalin al'umma musamman masu amfani da fusahar ta yanar gizo wajen hada hadar kudi a fadin kasar Sin.
Ban da wannan, a halin yanzu akwai kimanin mutane miliyan 700 a kasar Sin da ke amfani da fusahar yanarfannin lamarin da yasa kasar ta zamanto kan gaba a fagen amfani da yanar gizo a fadin duniiya. Har ila yau, kasar Sin na mallakar kamfani mafi girma a duniya a fannin dillancin kaya ta hanyar yanar gizo, wato kamfanin Alibaba. A ra'ayi na, wadannan dalilai sun isa baiwa kasar Sin wani matsayi na musamman kan wannan harka ta yanar gizo a duniya, kuma ina ganin shi ne ya karfafa wa kasar Sin gwiwar daukan nauyin shirya wannan babban taro na masu ruwa da tsaki kan fusahar yanar gizo da nufin kara inganta ta da tsaftaceta da kuma samar da cikakken tsaro ga wannan fanni.
Ina fatan masu ruwa da tsaki kan wannan batu za su bullo da wasu sabbin manufofi da matakai wanda za su tsaftace harkar yanar gizo a duk fadin duniya. Ina kuma jinjinawa shugaba Xi Jinping bisa gabatar da jawabi mai karsashi yayin bude taron.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Shugaban kungiyar
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria