in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron G20 a birnin Hangzhou ya sami nasara!
2016-09-13 08:55:50 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI, Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa dafatan maaikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya. Bayan ina mai alfaharin turo muku wannan sako tare da farin cikin bayyana muku cewa na bibiyi taron da gudana kwananan na kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 A birnin Hangzhou na kasar Sin, a gaskiya wannan taro yasami nasara sosai ganin yadda a gudanar da wasu mahimmam abubuwa a wannan, banban abin dayafi jan hankalina shine bayanin mai masaukin baki shugaban kasar Sin wato Xi Jinping inda yakuma jawo hankalin kasashe akan yadda zaa ceto tattalin arzikin duniya daga mawuyacin halin daya shiga musamman tashare shinge da fadada kasuwanci da kirkire kirkire da sauransu. Wani abu daya kuma jaho hankalina shine yadda akayi kira gurin taimakawa kasashen Afirka domin su bunkasa tattalin arzikinsu, kodayake a yanzu kasar Sin ta cancanci yabo ganin yadda tafi kowace kasa zuba jari a kasashen Afirka. Banda haka naji dadin shirinku na yau na Allah daya gari banban wanda kukayi cikaken bayani kan taron G20 na garin Hangzhou.

Akarshe inasan yin amfani da wannan dama gurin taya alummar Musulmi murnar yin Aikin Hajji na bana Allah yasa ayi lafiya agama lafiya. Haka kuma inaiwa masu sauraro murnar bikin babbar sallah wacce zaayita ranar Litinin. Allah maimatamana Ameen. Nagode

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, Great Wall CRI Listeners Club Kano State Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China