A cikin tsawon lokacin da na dauka ina sauraren tashar CRI (kimanin shekaru 29 da suka wuce), ina iya cewa, na karu sosai domin na samu karin ilimin da watakila ban samu ba ko da kuwa a makaranta ne. Yayin da alakata da CRI ta taimaka mini ainun wajen kara samun abokai da aminai a nan Najeriya da ma wasu kasashen Duniya. Na kuma fahimci abubuwa masu tarin yawa game da kasar Sin da kyawawan al'adun Sinawa.
A hakikanin gaskiya kasar Sin ta yi tasiri sosai a kasashen Duniya, tasiri wadda ba zai misaltu ba domin girma da yawa, sai dai a kimanta ko a takaita. Amma dai saboda wannan gasa na CRI, zan so in yi bayani daidai yadda hankali zai aminta da shi wato a zahirance.
Garemu masu sauraren CRI, muna iya faro bayanin daga kokarin CRI saboda sanin yanayin gudunmuwar da CRI ya bayar a cikin shekaru 75 da kafuwarsa wajen tallata kasar Sin a idanun Duniya domin kowa ya san kasar da abinda kasar ta kunsa a bangarori masu yawa, da kuma yanayin bunkasa da Sinawa suke samu a kullum.
A can baya, cikin tarihi, kasar Sin ta fuskanci wahalhalu na yake-yake, amma kwanci-tashi sai Allah Yasa ta samu shugabanni na kwarai masu hangen-nesa, Wadannan shugabanni su suka aza kasar bisa tubali mai karfi wajen sanya kasar a kan hanya mai nagarta kuma mikakka har ta kai yadda take a yau.
Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ta yi fice ainun a fannoni masu dama wadanda suka hada da kimiyya da fasaha da kere-kere da noma irin na gargajiya da na zamani domin ciyar da kanta. A zahirance, muna iya ganin na'urorin kwamfuta daban-daban a yankunanmu wadanda muke amfani da su yau da kullum, ga wayoyin hannu na salula da tufafi kala-kala da takalma da littattafai da jakkuna da motoci da jiragen kasa da na sama da kayayyakin alatu na daki da kwanukan girki da na abinci da magunguna na zamani da na gargajiya da wasu miliyoyin kayayyaki wadanda wannan rubutu ba zai dauke su ba, wadannan abubuwa duk da taimakon kasar Sin ne suka zama masu sauki wajen farashi ta yadda galibin masu karamin karfi kan iya saye ba tare da kuntata ba.
A galibin kasashenmu na Afirka, muna iya cewa, kasar Sin har kullum tana bayar da muhimman gudunmuwa a bangarori daban-daban na rayuwa, kama daga raya karkara da taimakawa wajen kawo zaman lafiya ta hanyar tsaro da bayar da taimako a bangaren kiwon lafiyar al'umma da aiwatar da kwangiloli na gina gidaje da hanyoyi da asibitoci da filayen wasannin motsa jiki da ofisoshi da layin dogo da wutar lantarki da dai sauransu. Ashe kenan kasar Sin tayi tasiri a wadannan bangarori.
A hakikanin gaskiya, kasar Sin tayi tasiri, kuma tana kan yin tasiri a idanun al'ummar yankina na Arewacin Najeriya fiye da tunanin dan-Adam. Na yi amanna babu gida a yankin Arewacin Najeriya da babu kaya kirar kasar Sin a ciki. Kuma na tabbata miliyoyin al'ummar Najeriya sun fi amfani da kaya kirar kasar Sin fiye da na kowace kasa. Kenan, muna iya cewa, tasiri bisa tasiri kasar Sin ta yi a zukatan mutanen yankina da ma mutanen kasata baki daya a fannonin rayuwa masu dama a yau da kullum.
Bugu da kari, da taimakon CRI, mutane masu yawa daga nan kasata kan tafi kasar Sin domin saye da sayarwa domin ci gaba, kuma harkar kasuwanci yayi karfi a tsakanin juna har kuma ana cin moriyar juna.
Allah Ya taimaka.
Salisu Muhammad Dawanau
9 ga Satumba, 2016