lafiya1533.m4a
|
Masu nazari da suka fito daga kasashen Canada da Amurka, sun gabatar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, wanda ke nuna cewa idan kananan yara suna sauraron kide-kide yayin da ake yi musu allura, to, hakan zai sassauta ciwon da zasu ji kadan, ta yadda za su samu jinya yadda ya kamata.
Masu nazari daga jami'ar Alberta da sauran cibiyoyin nazari na kasar Canada, sun tantance kananan yara 42 da ake yiwa jinyar gaggawa a wani asibiri da ke lardin Alberta, wadanda daga cikin su wasu suke sauraron kide-kide yayin da ake yi musu allura, wasu kuma ba su saurara ba. Bayan da aka yi musu jinya, masu nazarin sun yi bincike kan yadda suke jin ciwo yayin da suke samun jinya.
Masu nazarin sun gano cewa, a bayyane kananan yaran da ba su saurari kide-kide ba yayin da ake yi musu allura, sun fi jin ciwo idan aka kwatanta da wadanda suka saurari kide-kiden yayin da ake yi musu allura. Ban da haka kuma, a cikin kananan yaran da suka saurari kide-kide yayin da ake yi musu allura, masu aikin jinya da yawansu ya kai kashi 76 cikin dari ne suka nuna cewa, wadannan kananan yara sun fi ba da nasu taimako yayin da suke yi musu allura. Masu aikin jinya ba su gamu da wata matsala ba wajen yi musu allura. Amma a cikin kananan yaran da ba su sauraron kide-kide yayin da ake yi musu allura, masu aikin jinya da yawansu ya kai kashi 38 cikin dari ne kawai suka nuna cewa, ba su gamu da wata matsala ba wajen yi wa wadannan kananan yara allura.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, samar da kide-kide yayin da ake jinyar kananan yara, wata kyakkyawar hanya ce mai arha kuma mai sauki wajen ba da jinya, wadda kan samar da babban sakamako. Za kuma a ci gaba da yin nazari kan ko samar da kide-kide, da sauran hanyoyin da za a iya bi za su taka rawa wajen karkata hankalin kananan yara yayin da ake ba su jinya, baya ga yi musu allura kadai. (Tasallah Yuan)