lafiya1523.m4a
|
Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya bayyana cewa, gwada yawan sinadaren da jikin mutum ke fitarwa yana iya tabbatar da ko wannan mutum ya kamu da ciwon sukari na 1 ko a'a. Ana sa ran cewa, za a yi amfani da sakamakon nazarin wajen tabbatar da kamuwa da ciwon sukari cikin gajeren lokaci kuma ba tare da mutum ya ji wani ciwo ba.
Yanzu haka ana tabbatar da ko mutum ya kamu da ciwon sukari ko a'a ne ta hanyar binciken jininsa, koda ya ke hakan na da bata lokaci sosai, haka kuma yara su kan ji ciwo sosai a lokacin da ake daukar jinin nasu. Masu nazari daga jami'ar Oxford sun wallafa wani rahoto a jaridar "nazari kan yadda dan_Adam ke numfashi", inda a cewarsu, bayan da suka gwada jinin kananan yara da matasa 113, wadanda shekarunsu suka kai 7 a duniya, amma ba su kai sheakru 18 ba, da kuma yadda suke numfashi, an gano cewa, sinadaren da masu fama da ciwon sukari nau'I na 1 suke fitarwa ya fi na masu koshin lafiya yawa. Da ma an tabbatar da wadannan masu fama da ciwon sukari nau'I na 1 sun kamu da ciwon ta hanyar binciken jininsu.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, idan yawan sinadarin Insulin da ke sarrafa ko daidaita yawan sukarin da ke cikin jinin bil-Adama ba shi da yawa a cikin jikin mutum, ba zai iya sarrafa kara karfin sanadarin Glucose da ke cikin jinin ba, a maimakon haka sai mitun ya fara ramewa. Kuma sinadaren da jikin bil-adam ke fitarwa(Ketone) suna daya daga cikin abubuwan da suke haddasa ramewar mutum. Haka nan Sinadarin Acetone shi ma yana daya daga cikin sinadaran da jikin mutum yake fitarwa
Bisa sakamakon wannan sabon nazari, yanzu masu nazarin suna nazarin wata na'ura wadda mutum zai iya rike ta a hannunsa. Nan gaba ana sa ran cewa, za a saukaka da kuma kara saurin tantance ko wani ya kamu da ciwon sukari nau'I na 1 ko a'a. Har wa yau kuma, masu fama da nau'I na farko na ciwon sukari da kuma mutanen da ke fuskantar babbar barazanar kamuwa da ciwon za su iya kara sanin halin da suka ciki wajen fama da ciwon, ta hanyar sanin yawan sinadarin Acetone da ke cikin jikinsu cikin lokaci kuma ba tare da sun je asibiti ba. (Tasallah Yuan)