in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahaifa mata masu yawan kiba kan kara wa jariransu barazanar mutuwa
2015-08-02 11:09:50 cri

Matsalar yawan kiba kan yi illa a fannoni da dama. Wani sabon nazarin da aka yi a kasar Birtaniya ya nuna cewa, idan nauyin jikin mata ya wuce misali, ko kuma suna kan sahun masu kiba kafin su samu ciki, ko kuma a farkon wa'adinsu na samun ciki, hakan zai sanya su fuskantar barazanar zubewar ciki, ko kuma mutuwar jariran da suke dauke da shi, ko mutuwar jariran bayan sun haife su. A cikin irin wadannan mata, nazarin ya ce idan masu juna biyun suna kan sahun masu kiba, to barazanar da za su fuskanta tana bisa matsayin koli.

A ko wace shekara, jarirai kimalin miliyan 2 da dubu dari 7 suna mutuwa yayin haihuwar su a dukkanin fadin duniya. Kana kuma jarirai kimanin miliyan 3 da dubu dari 6 suna mutuwa a cikin kwanaki 28 bayan da aka haife su.

Masu nazari daga kwalejin koyon kimiyya da fasaha a birnin London na kasar Birtaniya, sun tantance nazarin ilimin likitanci guda 38 masu ruwa da tsaki da aka yi a baya, a kokarin gano alakar da ke tsakanin mizanin BMI na awon nauyin mutum, da kuma batutuwan zubewar ciki, da mutuwar jarirai yayin da aka haife su, da mutuwar jarirai bayan da aka haife su.

Masu nazarin sun gano cewa, dan karuwar mizanin BMI na masu juna biyu, na karawa matan fuskantar barazanar zubewar ciki, da mutuwar jarirai yayin da suka haife su, da mutuwar jarirai bayan da suka haife su. Har ila yau matan da ke kan sahun masu kiba sun fi fuskantar irin wannan barazana. Binciken ya nuna cewa idan mizanin BMI na wata mace ya kai 40, to irin barazanar da take fuskanta ta fi wadda mizanin BMI nata yake 20 da rubi 2 zuwa 3.

Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram, idan an raba da tsayin mutum a mita sikwaya. Matsakaicin mizanin BMI na mutane na tsakanin 20 zuwa 25. Idan ya wuce 25, to, nauyin jikin mutum ya wuce misali, yayin da idan ya wuce 30, mutumin yana kan sahun masu kiba.

Duk da haka, masu nazarin sun nuna cewa, barazanar da matsalar kiba kan haddasa ga jarirai ta na yin kasa, gwargwadon barazanar da sauran matsaloli ke haddasawa. Alal misali, barazanar haihuwar matattun jarirai ga matan da mizanin BMI nasu ya kai 20 suke fuskanta ta kan kai kashi 0.76 cikin dari, irin wannan barazana ta kai kashi 1 cikin dari ga matan da ke kan sahun masu kiba, sa'an nan ta kai kashi 2.7 cikin dari ga matan da mizanin BMI nasu ya kai 40.

Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, wajibi ne a ba da jagoranci ga matan da ke shirin samun ciki, ta fuskar kiyaye nauyin jikinsu yadda ya kamata, a kokarin rage mutuwar jarirai yayin da suke cikin uwayen su, ko yayin da ake haifar su, ko kuma bayan an haife su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China