Ba zato, ba tsammani, hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria(INEC) bisa tallafin kasashen duniya da suka hada da: Sin, Amurka da kasashen taraiyar turai da kuma taimakon wasu kasashenmu na Afirka masu tasowa. Babu shakka kasashen duniya sun nuna kauna da fatan alheri bisa samun aiwatar da zabukan gama-gari cikin gaskiya da adalci wanda ya gudana a ranar asabar 28 ga watan Maris shekara ta 2015 a taraiyar Nigeria. Muna fata kasashen duniya ciki har da kasar Sin za su kara nuna kauna da kuma fatan alheri a zabukan gwamnoni da na yan majalisun dokoki na jihohi dake tafe a karshen mako mai zuwa 11 ga watan April. Madallah mun gode, Allah ya kara zumunci a tsakaninmu, amin. Kana ina kara godiya tare da babban yabo ga ma'aikatan sashin Hausa na Radio kasar Sin bisa babbar gudumowa da suke ci gaba da bayarwa wajen sanar da al'ummomin duniya hakikanin irin wainar da ake toyawa a zabukan gama-gari da aka fara a taraiyar Nigeria har zuwa yau lahadi da muke fatan kammala dukkan batutuwa da suka jibanci zabukan 2015.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.