lafiya1504.m4a
|
Mata masu dimbin yawa kan yi fama da ciwoce-ciwace ya yin al'ada su. A wannan lokaci kuma da daman su ba su son motsa jiki, sun fi son kasancewa a gidajensu kawai. Game da hakan wani masani daga kasar Jamus ya tunatar da mata cewa, tabbas dan motsa jiki kan na iya rage musu ciwon da ka iya damun su lokacin al'ada, ya kuma taimaka musu samun walwala da farin ciki.
Yayin da wannan shehun malamin da ke aiki a kwalejin ilmin motsa jiki na Cologne na kasar Jamus yake zantawa da kafofin yada labaru na kasar, ya bayyana cewa, motsa jiki kullum kan sassauta ciwon da mata kan ji kafin zuwan al'adarsu, da kuma lokacin zuwan al'adar. Ya ce ya yin da suke dan jin ciwon zuwan al'adar, baya ga taimakawa wajen warwarewar jijiyoyin jinni, motsa jikin yana kuma iya rage damuwa da matan su kan yi saboda rashin jin dadi a jikunansu.
Wannan shehun malami ya kara da cewa, hakika a lokacin zuwan al'adar mata, kazarkazar dinsu na motsa jiki na iya yin daidai da na yau da kullum, watakila ma ya dara na yau da kullum. Nazarin da aka yi ya nuna cewa, ga matan da aka yi musu bincike, sama da kashi 2 cikin kashi 3, kazarkazar dinsu na motsa jiki ta yi daidai da na yau da kullum, har ma ya dara na yau da kullum. Sai kuma adadin da bai wuce sulusi ba, wadanda kazarkazar dinsu na motsa jiki yana raguwa a lokacin zuwan al'adarsu.
Don haka wannan shehun malamin na kasar Jamus ya ba da shawarar cewa, a lokaci zuwa al'ada, kamata ya yi mata su dan rika motsa jiki bisa halin da jikunansu ke ciki, amma kada su motsa jikin fiye da kima. Saboda motsa jikin fiye da kima, zai iya haifar da motsalar haila, ko ma ya dakatar da zuwan ta baki daya.
A wani batun mai alaka da wannan, mata masu yawa kan yi saurin hasala, ko mutsu-mutsu, ko damuwa, ko kuma su rika jin ciwo a mamansu, akwai kuma masu yawan jin gajiya kafin zuwan al'adarsu, lamarin da ake kira "larurori da mata ke fuskanta kafin zuwa al'adarsu" wato PMS a Turance. Game da hakan wasu masu nazari na kasar Japan sun gano cewa ciwon PMS kafin zuwan al'ada, na sanya mata kara tsanar abubuwan da dama can ba sa son su. (Tasallah)