Babu shakka, taron kasa da kasa na dandalin hadin guiwar tattaunawar tattalin arzikin kasashen Asia da tekun Pacific ya ja hankalin kasa da kasa da kuma mu masu sauraro, bisa la'akari da cewa, Sin tana da babban dalili da damar yin tasiri cikin karko wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya ganin yadda kasar Sin suka dukufa kai da fata wajen ganin an samu sawaba da daidaito bisa lumana da fahimtar juna cikin yakini bisa nagarta a batun bunkasuwar tattalin duniya da kasashen Apec. Kana, na gamsu da kalaman da tsohon firaministan kasar Australia mr. Bob Hawke ya yi, a sa'ilin da yake jawabi a gun taron kasa da kasa akan dandalin hadin gwiwar taunawar tattalin arzikin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pacific a birnin Beijing na kasar, inda mr. Bob ya bada shawarar da a fito da wani tsari da zai kara ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta zamani a yankin Asiya da tekun Pacific. Kasar Sin dai kasa ce da ta himmatu sosai wajen samar da bunkasuwar tattalin arziki da yaukaka zaman lafiya a duniya, Sin tana bin nagartattun tsare-tsare mai kyau mai inganci wajen kiyaye zaman lafiya a yankin Asia da tekun Pacific da ma daukacin kasashen duniya baki daya. Kazalika, ina mai fatan cimma manyan buruka da nasarori da makasudun shirya taron dandalin tattaunawar kasashen APEC na bana a 2014 a birnin Beijing na kasar Sin, da fatan taron na bana zai zama wani muhimmin batu da zai kara ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasashen kungiyar APEC da kasar Sin ke sa muhimmanci wajen shiryawa da daukan nauyi da cimma nasarori masu yawa a taron APEC na birnin Beijing na kasar Sin. Har wa yau, ina mai nuna gamsuwa ta da karfafa tsaro a birnin Beijing dan bada kariya da inganta sha'anin tsaro sosai yayin da jiragen ministocin kudi da kasuwanci da shugabannin kasa da kasa da suka halarci taron apec bisa gaiyatar da kasar Sin suka yi musu.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.