in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a mai da hankali kan abincin da kananan yara suke ci, a lokacin da suke fama da tari
2014-06-09 09:23:15 cri
Hausawa kan ce, yara manyan gobe ne. Sinawa kan siffanta yara a matsayin kyakkyawar makomar ko wace kasa. Don haka yau a cikin shirinmu za mu ba da wasu shawarwari ne ga iyayen yara game abincin da ya kamata 'ya 'yansu su ci a lokacin da suke fama da tari.

Bayan da kananan yara suka kamu da cututtukan da ke da nasaba da numfashi, a wannan lokaci, idan iyaye suka mai da hankali kan abincin da yaransu su rika ci a zaman yau da kullum, hakan zai taimaka wajen warkar da tarin da yaransu ke fama da shi.

Da farko, ya kamata iyayen su shirya abincin da ba sa gishiri da kuma maiko sosai, amma ya fi kyau a zabi kayayyakin abinci masu gina jiki, da kuma yaran za su iya hadiye su cikin sauki, kamar kunun da aka dafa da kayan lambu da romo da dai sauransu.

Na biyu kuma shi ne, su rika matsa wa yaransu suna kokarin shan ruwa a maimakon lemo. Isasshen ruwa zai taimaka wajen sassan jikin yaran da suke fama da tarin.

Na uku kuma shi ne, kamata ya yi yaran su rika cin danyen kayan lambu da 'ya 'yan itatuwa. Danyen kayan lambu da 'ya 'ya itatuwa su kan ba da isassun gishiri dangin sinadarai masu gina jiki kamar sinadarin bitamin, wadanda suke taimakwa wajen warkar da tarin. Haka kuma, cin kayan lambu da 'ya 'yan itatuwa da suka hada da tumatir da karas da kuma abincin da ke dauke da bitamin A ya fi taimakawa wajen kyautata hanyoyin numfashi na yaran.

Na karshe shi ne, ya kamata yaran da suke fama da tarin su guji cin abinci mai gishiri ko kuma mai zaki. Abinci mai gishiri kan tsananta tari, abinci mai zaki kuma kan haifar da kaki, saboda haka ya kamata yara su yi kokarin kaucewa cin irin wannan abinci. Sa'an nan kuma, kada yara su ci abinci mai yaji, soyayyen abinci, abinci mai sanyi, da abincin teku. Haka kuma, ya fi kyau a hana yaran da suke fama da tarin cin soyayyen gyada da kankana da makamatansu.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China