A yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da tsohon shugaban kasar Kazakhstan, kuma shugaban kasar na farko, Nursultan Nazarbayev, inda ya ba shi lambar girma ta Zumunta, wadda ita ce lambar yabo mafi girma da gwamantin kasar Sin ta kan ba wani dan kasar waje.
Bayan da ya karbi lambar, mista Nazarbayev ya ce wannan lambar ta nuna yadda kasar Sin take yarda da kokarin da ya yi don kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2. A cewarsa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, ta riga ta zama wani dandali mai kyau ga bangarorin duniya da ke sha'awar hadin kai da juna. Shawarar, a cewar tsohon shugaban Kazakhstan, ta sanya kasashen nahiyoyin Asiya da Turai samun damar bai daya ta raya kansu, gami da taimakawa tabbatar da zaman lafiya da walwala a duniya. (Bello Wang)