Shugaba Xi ya yi bayanin cewa, yayin taron kolin a wannan rana, bangarori daban daban sun cimma daidaito kan raya shawarar "ziri daya da hanya daya" mai kyautatuwa, wadanda aka rubuta su a cikin hadaddiyar sanarwar da aka fitar a gun taron. Sanarwar za ta kasance shirin kara hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa don raya shawarar "ziri daya da hanya daya".
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da ake shiryawa da gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar, bangarori daban daban sun cimma daidaito kan fannoni 283, ciki har da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, da fara yin hadin gwiwa a manyan fannoni, da kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, da gabatar da rahoto game da ci gaban da aka samu wajen raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da gabatar da rahoto game da shawarwarin da aka bayar a kwamitin bada shawara na dandanlin tattaunawar da sauransu. A matsayin kasa mai shugabantar taron kolin, kasar Sin za ta tsara wani jerin sunayen sakamakon da aka cimma. Wadannan sakamako sun shaida cewa, aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya" ya dace da yanayin duniya na yanzu, da kawo moriya ga dukkan duniya, da kuma amfanawa rayuwar jama'a. (Zainab)