in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Rasha da Sin sun zanta da juna
2019-04-26 19:45:07 cri

A yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka zanta da juna, a gefen taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu ko BRF a takaice, wanda ke gudana a nan birnin Beijing.

Da yake tsokaci, shugaba Xi ya ce Rasha muhimmiyar kawa ce dake cikin jerin bangarori da suka rungumi shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI. Shugaba Xi ya ce, daidaita shawarar ziri daya da hanya daya da kudurorin dandalin raya tattalin arzikin Turai da Asiya, tsari ne mai nagarta, na raya hadin gwiwar tattalin arzikin yankuna.

Ya ce, ya kamata bangarorin biyu, su ci gaba da fadada hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da samar da makamashi, da binciken kimiyya da fasaha, da bangaren binciken sararin samaniya, da hade sassan duniya, baya ga hadin gwiwa a matakai na kasashe, da musaya tsakanin al'ummu da al'adu.

Shugaba Xi ya kuma kara da cewa, Sin za ta aike da dabbobin panda biyu zuwa kasar Rasha, domin gudanar da binciken hadin gwiwa tsakanin masana na sassan kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaba Putin ya ce shawarar ziri daya da hanya daya, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ta samar da muhimmin dandali na hadin gwiwa, tare da kasancewa misali mai ma'ana a fannin fadada hadin gwiwar kasa da kasa, ta kuma kara samun karbuwa daga sassan kasa da kasa. Ya ce, yadda shugabannin kasashen duniya masu tarin yawa suka halarci dandalin, ya nuna sahihancin wannan batu da ya yi.

Shugaban na Rasha, ya kuma ce a wannan gaba da kasashen Sin da Rasha ke cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya da juna, Rasha na da nufin kara inganta kawancenta da Sin, da zurfafa musaya tsakanin su a fannoni da dama, kamar fannin aiwatar da manyan ayyuka da suka shafi makamashi, da hade sassan ci gaba masu tarin yawa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China