Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a jiya, da sakatare janar na MDD Antonio Guterres, wanda ke halartar taro na 2 na dandalin tattaunawa hadin kan kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya, dake gudana a nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya ce, kasar Sin na martaba hadin gwiwar kasa da kasa bisa ka'idojin MDD da kuma dokokin kasa da kasa, tare da inganta gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil adama.
Shugaban wanda ya ce ba kokarin kyautata rayuwarsu kadai al'ummar Sinawa ke yi ba, har ma da aiki domin cimma bukatu na bai daya na al'ummar duniya, ya ce shawarar ziri daya da hanya daya, na kunshe da alfanu na moriyar juna kuma ta dace da tsarin MDD na muradun ci gaba masu dorewa.
Da yake bayyana MDD a matsayin muhimmiya wajen yayata shawarar, shugaba Xi ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki da MDD wajen inganta shawarar ta kowacce fuska bisa ka'idar samar da alfanu na bai daya ta hanyar zurfafa tuntuba da hadin gwiwa.
A nasa bangaren, Antonio Guterres, jinjinawa manyan matakan kasar Sin na kara bude kofa da aiwatar da gyare-gyare ya yi.
Kana da yake kira ga kasashen duniya su yi amfani da damar dake tattake da hadin gwiwa karkashin shawarar don samun sakamako na moriyar juna, Guterres ya ce, tarihi zai nuna cewa, yanayin ci gaban kasar Sin ba muhimmin abu ne da za a iya yin biris da shi ba kadai, domin babbar gudunmuwa ce ga ci gaban bil adama. (Fa'iza Mustapha)