Jiya Talata, MDD ta kira babban taron tunawa da "ranar kasashen duniya ta goyon bayan al'ummar Palestinu", shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sako domin taya murna.
A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, batun da ya shafi Palestinu yana da muhimmanci matuka a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda ya shafi zaman lafiya a yankin, shi ya sa wajibi ne a kara mai da hankali kan batun. Kana ya kamata bangarori biyu wato Palestinu da Isra'ila su yi hakuri da juna domin gujewa kara tsananta yanayin siyasa a yankin. Ban da wannan kuma, sauran sassan da abin ya shafa su yi hangen nesa su yanke shawarar siyasa da ta dace cikin sauri, da haka za a maido da shawarwarin zaman lafiya tun da wur wuri. Kasar Sin tana maraba da kuma goyon bayan daukacin kokarin da ake domin sassauta yanayin da yankin ke ciki.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana goyon bayan sha'anin al'ummar Palestinu, tana kuma yin kokari domin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Kana bisa matsayinta na zaunannen mambar majalisar tsaron MDD, kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashen duniya domin cimma burin tabbatar da zaman lafiya bisa tushen adalci daga duk fannoni kuma cikin dogon lokaci a yankin Gabas ta Tsakiya.(Jamila)