Yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda Xi ya jaddada cewa, Masar kasa ce mai jagorancin kungiyar tarayyar Afirka wato AU a yanzu, kuma zuwan shugaban kasar nan Beijing domin halartar dandalin koli kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 ya nuna cewa, Masar tana dora muhimamnci matuka kan aikin gina shawarar. Ya kuma ce kasashen Afirka, suna himmantu wajen ci gabansu bisa tushen moriyar juna, kana har kullum kasar Sin tana goyon bayan Masar, a fannin nemi wata hanyar raya kasa da ta dace da yanayin da kasar ke ciki, tana kuma son shiga shirin raya yankin kogin Suez, haka kuma za ta ci gaba da ingiza aikin gina yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a bakin kogin, tare kuma da gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, a bangarorin gina kayayyakin more rayuwa, da samar da kayayyaki da sauransu.
A nasa bangare, shugaba Sisi ya bayyana cewa, Masar tana son koyon fasahohin raya kasa da kasar Sin ta samu, tare kuma da tsara shirin raya kasarsa bisa la'akari da bukatun shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a kara zurfafa hadin gwiwa daga duk fannoni.(Jamila)