Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Chile Sebastian Pinera a Larabar nan a nan birnin Beijing, gabanin babban taron dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu dake tafe.
Yayin zantawar su, shugaba Xi ya ce ya kamata Sin da Chile su riki shawarar Ziri daya da hanya daya, a matsayin wata sabuwar dama ta zurfafa yarda da juna a fannin siyasa, da inganta hadin gwiwar su yadda ya kamata, su kuma ingiza kawancen su bisa manyan tsare tsare daga dukkanin fannoni.
Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su bunkasa hadin gwiwa a fannin cinikayya da zuba jari, su kuma karfafa hadin gwiwa a fannoni irin su hakar ma'adanai, da samar da makamashi mai tsafta, da fannin sadarwa, da cinikayya ta yanar gizo, da raya fasahohin kirkire- kirkire, da binciken yankuna masu tsananin sanyi.
A nasa tsokaci kuwa, shugaban kasar Chile cewa ya yi, kasar sa na da burin shiga a dama da ita wajen tabbatar da nasarar kudurorin dake kunshe cikin shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda hakan zai ba da damar hade sassan nahiyoyi daban daban.
Mr. Pinera, ya ce yana fatan kasar sa za ta yi koyi da kasar Sin a fannin ci gaban da sassan kirkire-kirkire suka haifar, da kuma wanda ake samu ba tare da gurbata muhalli ba. Kana ta yi hadin gwiwa da Sin wajen fadada hadin gwiwa a wadannan muhimman sassa.(Saminu)