in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci kasashen duniya su taimaka wajen samar da mulkin demokradiyya a kasar
2019-04-15 10:48:31 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan, ya bukaci al'ummomin kasa da kasa su mara baya ga kokarin kwamitin sojin kasar na tabbatar da samar da mulkin demokraddiya da ci gaba a kasar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce matakan da rundunar sojin kasar ta dauka sun dace da muradun jama'ar kasar, na samun 'yanci da adalci da zaman lafiya, bayan kiran da suka yi ga rundunar soji ta shiga tsakani domin kawo karshen tabarbarewar siyasa da tsaro da na zaman takewa a kasar.

Sanarwar ta kuma yi nuni da tabbacin da shugaban mulkin soji na riko ya yi cewa, za a mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru 2 masu zuwa.

Ma'aikatar ta jaddada cewa, kasar Sudan ta kuduri niyyar aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma a cikin kasar da yankin da take, da ma na kasa da kasa, da kuma shirin kyautata huldar makwabtaka da kuma huldarta da sauran kasashen duniya.

Ta kuma bayyana burin kasar na hada kai da kasa da kasa a bangaren raya tattalin arziki domin samun damar amfana daga dimbin albarkatun da take da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China