in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin soji ya soke dokar takaita zirga-zirga a Sudan
2019-04-14 16:06:18 cri
Shugaban kwamitin Soji na wucin gadi a Sudan, Abdel-Fattah Al-Burhan, ya sanar da soke dokar takaita zirga-zirga a kasar.

Cikin jawabinsa da gidan talabijin na kasar ya watsa kai tsaye a jiya Asabar, Abdel-Fattah Al-Burhan ya ce yana sanar da soke dokar takaita zirge-zirga da kuma sakin dukkan mutanen da aka kama karkashin dokar ta baci.

Ya kuma ayyana dakatar da dukkan gwamnonin soji da kuma mika ragamar ayyukansu ga kwamandojin soji dake jihohin.

Shugaban na rikon kwarya, ya kuma bayyana kudurinsa na kafa gwamnatin farar hula, wadda za ta rike ragamar mulkin kasar cikin shekaru biyu masu zuwa.

Ya kuma bayyana cewa za a kafa gwamnatin ne bisa tuntubar jam'iyyun kasar Sudan.

An nada Al-Burhan ne a ranar Juma'a, a matsayin sabon shugaban kwamitin soji, wanda ya maye gurbin Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf wanda ya sanar da yin murabus dinsa a wannan rana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China