Kungiyar ta yi kiran ne lokacin da ta gana da Abdel-Fattah Al-Burhan, shugaban kwamitin mulkin soji na kasar.
Daya daga cikin mambobin kungiyar Omer Al-Digair, ya bayyanawa manema labarai cewa, baya ga gwamnatin farar hula, suna bukatar a shigar da fararen hula cikin majalisar shugabancin kasar na wucin gadi.
Ya ce kungiyar za ta gabatar da jerin bukatunta ga shugaban na rikon kwarya a yau Lahadi.
Omer Al-Digair, ya kuma ce kungiyarsu ta bukaci kwamitin sojin ya sake fasalin hukumar tsaron kasar tare da hukunta dukkan wadanda ke da hannu a laifukan cin hanci da kashe masu zanga-zanga. (Fa'iza Mustapha)