A jiya Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban hukumar zartaswar EU Jean-Claude Junker, inda suka amince su karfafa alakar dake tsakanin Sin da EU, da ma yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa.
Shugabannin sun gana ne a kasar Faransa a gefen taron dandalin tafiyar da harkokin duniya da kasashen Sin da Faransa suka jagoranta tare.
Shugaba Xi ya kuma lura da yadda ake kara samun tashe-tashen hankula da nuna kariya ga harkokin cinikayya da yanayi na rashin tabbas a duniya. Ya ce, a shirye kasar Sin ta ke, ta yi aiki da sauran bangarori, ta yadda za a kare manufar cudanyar kasashen duniya, da inganta yadda ake tafiyar da harkokin kasa da kasa, da ma hada kai don magance kalubalen da duniya ke fuskanta.(Ibrahim)




