
Jiya Lahadi da dare ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, a birnin Nice na kasar Faransa.
A yayin ganawar, shugaba Xi ya nuna cewa, bana, shekaru 70 ke nan da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kana shekaru 55 da kulla huldar jakadanci a tsakanin Sin da Faransa. A daidai wannan lokaci da ya ke ziyara a Faransa, lamarin na da ma'ana ta musamman.
Xi Jinping ya jaddada cewa, tabbatar da kyakkyawar huldar da ke tsakanin Sin da Faransa, yana da muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar kasashen 2, kana zai yi muhimmin tasiri kan duniyarmu. Dole ne kasashen 2 su fadada fannonin yin hadin gwiwa a tsakaninsu, su habaka hadin gwiwarsu, su kuma kara kokarin aiwatar da shirye-shirye dake da alaka da shawarar "ziri daya da hanya daya" da samun sakamako cikin gajeren lokaci. Kasar Sin tana son ci gaba da inganta tuntubar juna da taimakawa juna ta fuskar harkokin MDD, yiwa kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO gyaran fuska, da matsalar sauyin yanayi da sauran muhimman batutuwa. Har ila yau kasar Sin na goyon bayan dunkulewar nahiyar Turai, tana kuma fatan Faransa za ta yi jagora da sa kaimi kan ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai.
A nasa bangaren, shugaba Macron ya ce, Faransa tana daukar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Ta kuma yaba da muhummiyar rawa da gudummowa da kasar Sin take bayarwa kan batun sauyin yanayi da sauran batutuwan kasa da kasa. Kasarsa tana son kara tuntubar kasar Sin da taimakawa juna wajen ganin huldar abokantaka a tsakanin Faransa da Sin bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni ta yi jagora wajen tabbatar da kasancewar rukunoni daban daban a duniya da kokarin samun zaman lafiya da wadata a duniya. (Tasallah Yuan)




