






A ranakun 24 da 25 ga wata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron suka gana da juna sau biyu cikin awoyi 24, inda suka yarda da raya kyakkyawar huldar abota a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni yadda ya kamata.
A ranar 25 ga wata, shugabannin 2 sun kalli yadda aka sanya hannu kan yarjeniyoyi guda 14 tsakanin kasashen 2.
Yayin shawarwarin nasu, shugaba Xi ya ce, dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da kasar Sin ta kaddamar a kwanan baya, za ta ci gaba da sassauta kayyadewar da aka yi kan ba da iznin shiga kasuwannin kasar Sin, kyautata yanayin kasuwanci, inganta kare 'yancin mallakar fasaha, da kara bude kofar Sin ga ketare. A nasa bangaren, shugaba Macron ya ce, kasarsa tana son halartar taron dandalin tattaunawar kolin hadin gwiwa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na 2 da kuma taron baje-kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na duniya karo na 2 da kasar Sin za ta shirya.
Yayin da shugabannin 2 suka gana da manema labaru, shugaba Xi ya sake yin karin bayani kan tunanin kasar ta Sin na raya kasa, inda ya ce, muna neman kawo wa jama'ar Sin alheri, amma ko kadan ba mu manta da nauyin duniya da aka dora mana ba. Ba bunkasuwar kasar Sin kawai muke kokarin samu ba, a'a, mun gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", muna fatan kasa da kasa za su aiwatar da ita tare, za su tattauna tare, za su ci gajiyarta tare, za su kuma samu moriya da ci gaba cikin lumana, ta yadda a karshe 'yan Adam za su ji dadin zaman tare. Wannan shi ne ainihin al'adun kasar Sin mai tarihin tsawon shekaru dubu 5. (Tasallah Yuan)




