Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, tarihi, da ilmin falsafa, da ilmin adabi, da ilmin fasaha na kasar Faransa sun jawo hankalina sosai. Ya furta sunayen mashahuran masana a fannin ilmin fasaha na kasar Faransa, kana ya sha yin amfani da kalmomi da jimloli da suka shafi al'adun kasar Faransa, hakan ya bayyana sha'awarsa kan al'adun Faransa.





